1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron sauyin yanayi a Poland

Abdul-raheem Hassan
December 2, 2018

Masu zanga-zangar nuna goyon bayan kare sauyin yanayi a Beljiyam, sun bukaci daukar matakan dakile dumamar yananyi a duniya.

https://p.dw.com/p/39IFz
Belgien Brüssel Demonstration gegen Klimawandel
Hoto: Reuters/F. Walschaertz

Kimanin kasashen duniya daban daban har 200 ne suka halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Ketowice na kasar Poland.

Taron na bana na fatan cimma matsaya tsakanin kasashen duniya kan samar da kudaden aiwatar da yarjejeniyar Paris na 2015, tare  da fatan aiki tare domin rage dumamar yanayi a duniya sakamakon fitar da hayaki daga masana'antu da ababen hawa.