1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude taron yini biyu na ministocin harkokin wajen kungiyar NATO

April 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0L

Kungiyar tsaro ta NATO ta bude kofar daukar sabbin membobi a cikin ta. A lokacin da ake bude taron yini biyu na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar a birnin Sofia, kakakin kungiyar NATO James Appathurai ya ce za´a ba da damar daukar kasashen Kuratiya, Macedoniya da kuma Albaniya a cikin kungiyar a taron kolin da zata yi a Riga a karshen wannan shekara. To amma ya ce kafin wannan lokaci ba za´a bawa wadannan kasashen goron gayyatar halartar taron kungiyar mai membobi kasashe 26 ba. Har yanzu kuma kungiyar ba ta tsayar da shawara ba kan yadda zata tinkari kasashen Ukraine da Georgia wadanda ke da aniyar shiga kungiyar. Wani muhimmin batu da taron na Sofia zai tattauna a kai kuma shine game da fadada huldar dangantaku tsakanin NATO da sauran kasashen duniya.