1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da shirin yaki da tsattsauran ra'ayi

Zulaiha Abubakar
May 16, 2019

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da Firaiministar New Zealand Jacinda Arden sun kaddamar da shirin yaki da tsattsauran ra'ayin addini a kafafen sadarwar zamani.

https://p.dw.com/p/3IaDs
Frankreich Paris | Emmanuel Macron, Präsident & Jacinda Arden, Premierministerin Neuseeland
Hoto: picture-alliance/abaca

Shugabannin sun bayyana cewar shirin zai mayar da hankali ne wajen tace batutuwan da suka kunshi tunzura al'umma, da kuma cusa tsauraran akidun da suke haifar da rikici tsakanin al'umma, bincike dai ya tabbatar da yawan sakwonnin kai tsaye da jama'a suka dinga turawa juna a lokacin harin wasu masallatai a kasar New Zealand a watan Maris ya kai miliyan daya da rabi cikin kankanin lokaci.


A makon da ya gabata ne shugaba Macron na Faransa ya gana da Mark Zuckerberg shugaban kamfanin Facebook , don tattauna hanyoyin amfani da fasahar sadarwa ta hanyoyin da suka dace.