1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke wasu 'yan adawan Zimbabwe uku

March 17, 2013

'Yan sanda sun bi wasu na hannun daman madugun 'yan adawa Morgan Tsvangirai har gidajensu tare da tasa keyarsu zuwa caji ofis ba tare da bayyana dalilai ba.

https://p.dw.com/p/17zBt
Hoto: Jekesai Njikizana/AFP/Getty Images

Jami'an 'yan sandan Zimbabwe sun cafke wasu na hannun daman firaministan Morgan Tsvangirai su uku a gidajensu da ke birnin Harare. Ba a dai bayar da dalilan danke su ba har ya zuwa yanzu. Amma dai ya zo ne kwana daya bayan zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki da aka gudanar. Magoya bayan Tsvangirai sun saba fuskantar barazana daga bangaren jam'iyar da ke mulki, duk kuwa da kasancewarsa firaminista na gwamnati da ke ci yanzu. Ko gabanin wannan zaben ma sai da magoya bayan Robert Mugabe suka far wa wasu kusoshin jam'iyar adawa ta MDC.

Idan sakamakon zaben da aka kada gudanar a jiya asabar ya nunar da cewa 'yan Zimbabwe sun yi na'an da sabon kundin tsarin mulki, to dai za a kayyade wa'adin shugabancin kasa zuwa shekaru biyar so biyu. Sai dai kuma bisa ga sabon kundin tsarin mulki, Robert mugabe mai shekaru 89 da haihuwa, wanda kuma ya shafe shekaru 33 akan karagar mulki na da ikon tsayawa takara.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

AFP