1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto wasu 'yan ci rani a Girka

Abdullahi Tanko BalaAugust 17, 2016

Sojoji masu tsaron gabar ruwa a Girka sun ce sun ceto 'yan gudun hijira fiye da 300 cikin kogin Agean.

https://p.dw.com/p/1Jjw6
Schlauchboot mit Flüchtlingen
Hoto: picture alliance/dpa/G. Fischer

An ceto mutanen kwanaki tara da suka wuce, yayin da kuma sojojin na Girka suka ce sun sami nasarar ceto wasu 'yan gudun hijirar 59 a kusa da tsibirin Kos. Hakan nan kuma sojojin sun kama wasu mutum biyu masu safarar mutane tare da kwace jiragen ruwa guda hudu. Galibin jiragen ruwan da ake safarar mutanen jirage ne marasa inganci inda kuma a yawancin lokuta su kan kife da mutane.