An cika shekaru biyu da fara kaɗawar guguwar neman sauyi a Tunisiya
December 17, 2012A wannan Litinin, al'umar Tunisiya suka fara bikin cikar shekaru biyu da ɓarkewar zanga-zangar juyin-juya hali, wadda ta kifar da mulkin shugaba Zin El-Abedine ben Ali, sannan ta bazu zuwa sauran ƙasashen larabawa.
Shugaban ƙasa Moncef Marzouƙi da shugaban Majalisar Dokoki Mustapha Ben Jaafar, sun halarci garin Sidi Bouzid, dake matsayin cibiyar zanga-zangar, to saidai duban mutane sun tarbe su da ihu da jifa da duwatsu,tare da zargin su da cin amanar juyin-juya hali.
Mohamed Ali shine shugaban ƙungiyar gwagwarmayar ci gaban Sidi Bouzid ya yi huruci ya na cewa:
" Ba su yi komai ba,illa neman kuɗi su cika alhifansu.
Sam! ba su damu da halin da talaka ke ciki ba.Su da kansu sun yi imanin cewar basu tsinana wani abin azo a gani ba, a cikin wannan shekaru biyu".
Dubun-dubatar mutanen da suka hallara a dandalin ƙwatar 'yanci, sun yi ta rera kalamomi masu buƙatar shugabanin su yi murabus.
Jama'a da dama a ƙasar Tunisiya na zargi magabatan da kasa tabura komai, domin magance manyan ƙalubale da ƙasa ke fama da su, hasali ma rashin aiki yin da talauci.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman