1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma matsaya a taron canjin yanayi na Bali

December 15, 2007
https://p.dw.com/p/Cc60

Shugabannin ƙasashen duniya wajen taron canjin yanayi a Bali sun cimma daidaito a ƙurerren lokaci ,inda suka tsara sabbin hanyoyi da za a bi don samarda sabuwar yarjejeniya kan ɗumamar yanayi. Bayan tattaunawa mai zafi na sao’i da dama da tun farko aka zaci ba za a samu nasara ba,yanzu haka kusan dukkan ƙasashe 190 da suka halarci taron sun amince da sabuwar taswirar da zaa bi don cimma sabuwar yarjejeniyar a 2009. An dai samu wannan nasara ce bayan Amurka ta janye adawa da takeyi da shirin ta kuma amince da shawarar da ƙasashe masu tasowa suka bayar. Sabuwar yarjejeniyar zata maye gurbin yarjejeniyar Kyoto bayan ƙarewar wa’adinta a shekara ta 2012.