1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma matsaya kan kasafin kudin Amurka

Usman ShehuJanuary 2, 2013

'Yan majalisar wakilan Amurka da gwamnatin Shugaba Barack Obama sun cimma matsaya kan bukatar shugaban ta kaucewa karawa mutanen da ke da matsakaicin karfi haraji.

https://p.dw.com/p/17C9f
WASHINGTON - NOVEMBER 16: U.S. President Barack Obama (R) shakes hands with Speaker of the House John Boehner (R-OH) during a meeting with bipartisan group of congressional leaders in the Roosevelt Room of the White House on November 16, 2012 in Washington, DC. Obama and congressional leaders of both parties are meeting to reportedly discuss deficit reduction before the tax increases and automatic spending cuts go into affect in the new year. (Photo by Olivier Douliery-Pool/Getty Images)
USA - Präsident Obama trifft sich mit führenden Kongress-AngehörigenHoto: Getty Images

Amincewa da wannan bukata ta shugaba Obama da 'yan majalisar wakilan su ka yi dai ta biyo bayan shafe tsawon lokaci ana kiki-kaka tsakanin bangaren majalisar dokokin kasar wanda galibinsu 'yan jam'iyyar Republican ne da kuma da kuma bangaren zartarwa.

John Boehner Sprecher der Republikaner USA Dezember 2012
Kakakin majalisar wakilan Amurka John BoehnerHoto: Getty Images

'Yan majalisar dai a baya sun tsaya kai da fata wajen kin amincewa da bukatar ta shugaba Obama dangane da wannan batu inda daga bisani bayan su ka dau tsawon lokaci su na tattaunawa har su ka kai ga cimma matsaya har ma aka kada kuri'ar amincewa da kudurin.

'Yan majalisa dari biyu da hamsin da bakwai ne dai su ka amince da wannan kuduri yayin da dari da sittin da bakwai su ka kada kuri'ar rashin amincewarsu.

Da ya ke jawabi jim kadan bayan mafi rinjaye na 'yan majalisar su ka amince da kudurin, Shugaba Obama ya jinjinawa 'yan jam'iyyarsa ta Democrat da kuma abokan hammayarsu na Republican dangane da cimma wannan matsaya.

Shugaba Obama ya ce ''na godewa 'yan majalisarmu na jam'iyyar Democrat da na Republican dangane da kada kuri'ar amincewa da wannan kuduri. Zan sanya hannu kan dokar da za ta amince da kara haraji ga attajiran Amurka wanda da yawansu bai wuci kashi biyu ciki dari na Amurkawa ba, yayin da a hannu guda dokar za ta kaucewa kara haraji ga masu matsakaicin karfi wanda zai kai ga jefa tattalin arzikinmu cikin tsaka mai wuya gami da shafar iyalai da dama.''

To baya ga batun na karawa attajirai haraji da majalisar ta amince da shi, a hannu guda kuma bangarorin biyu sun amince da batun rage kudaden da gwamnatin kasar ke kashewa, daya daga cikin irin abubuwan da 'yan jam'iyyar Republican ke son ganin shugaban ya amince da shi.

Repräsentantenhaus Wahl Abstimmung Legislatur Fiskal Klippe USA Washington
Majalisar dokokin AmurkaHoto: Getty Images

''Ya ce dukannin mu mun shaida cewar wannan dokar wani mataki ne na yunkurin da mu ke na karawa tattalin arzikinmu tagomashi da kuma samar da damammaki ga kowa da kowa. Sai dai gibin da ake da shi na kasafin udi fa har yanzu ya na da yawa kuma ba mu yi abubuwa na a zo a gani wajen gani ba wanda za su taimaka wajen ciyar da tattalinmu arzikin gaba.''

Da ya ke tsokaci dangane da wannan batu, dan majalisa Tom Cole da ke zaman dan jam'iyyar hammaya ta Republican ya ce duk da an amince da wannan batu, dole ne fa sai an tashi tsaye wajen daidaita al'amura domin kaiwa ga ci.

USA Haushaltstreit Steuerstreit Fiskal Klippe Mitch McConnell
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka Mitch McConnellHoto: Getty Images

Ya ce ''ba lallai ne 'yan majalisar dattawa su amince da batun rage kudaden da ake kashewa a gwamnatance ba amma ina ga dole ne mu yi aiki dangane da wannan batu a yau din nan.''

Masu fashin bakin siyasar a Amurka dai na ganin cewar wannan cigaban da aka samu ya kawo karshen rajin da 'yan jam'iyyar Republican su ka ka shafe sama da shekaru goma su na yi na dakile karin haraji ga masu hannu da shuni kuma hakan a ganinsu na iya jawo koma baya ga cigaban siyasar madugun 'yan jami'iyyar ta Republican a majalisar wato John Boehner.

Nan gaba kadan ne dai ake sa ran shugaban na Amurka zai sanya hannu kan wannan doka wanda zai kawo karshen cece ku ce tsakanin shugaban da 'yan majalisar dangane da wannan batu.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman