1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma matsaya kan nukiliyar Iran

November 24, 2013

Iran da kasashen nan shidda da suka gudanar da tattaunawa a birnin Genevan kasar Switzerland kan shirinta na nukiliya sun cimma yarjejeniya cikin daren asabar zuwa lahadi.

https://p.dw.com/p/1ANDk
European Union foreign policy chief Catherine Ashton (3rd L) delivers a statement during a ceremony next to British Foreign Secretary William Hague, Germany's Foreign Minister Guido Westerwelle, Iranian Foreign Minister Mohammad Javad Zarif, Chinese Foreign Minister Wang Yi, U.S. Secretary of State John Kerry, Russia's Foreign Minister Sergei Lavrov and French Foreign Minister Laurent Fabius (L-R) at the United Nations in Geneva November 24, 2013. Iran and six world powers reached a breakthrough agreement early on Sunday to curb Tehran's nuclear programme in exchange for limited sanctions relief, in a first step towards resolving a dangerous decade-old standoff. REUTERS/Denis Balibouse (SWITZERLAND - Tags: POLITICS ENERGY) (eingestellt von qu)
Hoto: Reuters

Bayan da suka shafe tsawon lokaci suna gudanar da zazzafar muhawa, ministocin harkokin wajen Iran da Amurka da Birtaniya da China da Rasha da Faransa gami da kasar Jamus sun amince a kan dakatar da shirin nata na nukliya da kashi 20 cikin 100. Kazalika an amince cewar Iran za ta baiwa jami'an hukumar da ke sanya idanu kan harkokin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya dama don sa ido a wuraren da ta ke sarrafa makamashin Uranium, yayin da kasashen suka amince da sassautawa Iran din wani bangare na takunkumin da suka kakaba mata.

To sai dai ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya ce Iran din za ta ci-gaba da wani bangare na shirin nata na nukiliya wanda ya ke na zaman lafiya. Tuni da shugaban Iran Hassan Rouhani da takwaransa na Amirka Barack Obama suka yi na'am da wannan yarjejeniya ta wucin gadi da aka cimma,. Sai dai Izra'ila ta ce yarjejeniyar da aka cimma maras kyau ne.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe