An cimma sulhunta rikicin siyasar Amirka
October 17, 2013Shugaba Barack Obama na Amirka ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar. Majalisar Dattawa da na wakilan Amirka sun cimma yarjejeniyar kawo karshen tsayar da ayyukan gwamnati ne, domin kare kasar daga fadawa rcikin ikicin tattalin arziki, da zai iya hanata biyan basussukan da ke kanta. To sai dai yarjejeniyar da aka cimma ta kwarya kwarya ce, wadda bata magance wasu matsaloli na kashe kudade da gibi, da ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Demokrat da takwarorinsu na Republikan ba.
Shugaba Obama ya ce wannan abun farin ciki ne a gare mu " za mu fara bude ma'aikatunmu ba tare da bata lokaci ba. Kuma za mu kawar da wannan yanayi na rashin sanin tabbas kan harkokin kasuwancinmu dama tsakanin al'ummar Amurka. Akwai gagarumin aiki a gabanmu na dawar da martabar da muka kusan yin asararsa a bangaren Amurkawa".
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe