1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage shari´ar Saddam izuwa 12 ga Aprilu

Ibrahim SaniApril 6, 2006

Tsohon shugaban kasar Iraqi ya karyata zargin da ake masa na hannu a cikin kisan kiyashin shi´awa 148

https://p.dw.com/p/Bu0m
Hoto: DW

Ya zuwa yanzu dai rahotanni daga Iraqi, sun shaidar da cewa tsohon shugaban kasar ta Iraqi wato Saddam Hussain ya kauracewa zaman kotun na yau da aka dauki tsawon awowi biyu ana gudanarwa a birnin Bagadaza.

Duk da kin halartar kotun daga bangaren tsohon shugaban kasar ta Iraqi,tsohon alkalin daya yanke hukuncin kisan shi´awan nan 148 a shekara ta 1980, wato Awad Al Bandar ya karyata zargin cewa yayi gaggawa wajen yanke wannan hukunci a wancan lokaci.

Awad Al Bandar ya fadi hakan ne kuwa a zaman kotun na yau, lokacin da alkali, Raouf abdel Rahman da kuma masu gabatar da kara ke masa tambayoyi a game da cewa yabi son ra´ayin sa ne ta hanyar gaggauta yanke hukuncin kann wadannan shi´awa 148.

A lokacin da Awad Al Bandar ke jawabi ya tabbatar da cewa lauya guda daya ne daga bangaren gwamnati ya kasance yana kare shi´awan 148, a lokacin da ake sauraron shari´ar da ake musu na kokarin kisan shugaba Saddan Hussain.

Tsohon alkalin Awad Al Bandar dai na daya daga cikin mukarraban Saddan Hussain guda bakwai da ake zargin su da take hakkokin bil adama a lokacin zamanin tsohon shugaban na Iraqi.

Kafin dai dage zaman kotu a jiya laraba, sai da Saddam Hussain yayi watsi da hujjar da aka gabatar masa na cewa yana da hannu a cikin kisan kiyashin da akayiwa shi´awan 148.

Wadannan kalaman dai na Saddam Sun zo ne, kwana daya bayan an fito da wani sabon zargi da akewa tsohon shugaban na gudanar da kisan kiyashi kann yan kabilar kurdawa kusan dubu dari a lokacin mulkin sa.

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun nunar da cewa an dage zaman kotun na yau ne izuwa ranar 12 ga watan aprilun wannan shekara da muke ciki.

A wata sabuwa kuma yawan mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon tashin bom din a MAKABARTAR DA MANYA MANYA LIMAMAN YAN SHI´A SUKE a garin Najaf ,a yanzu haka sun kai 15,banda wasu kusan hamsin da suka jikkata.

Bom din dai ya tashi ne a dai dai kofar shiga makabartar da tsakar ranar yau din nan alhamis.

Ya zuwa yanzu dai tuni aka kaddamar da dokar ta baci a wannan guri a kokarin da jami´an tsaro keyi na ganin an tabbatar da doka da kuma oda.

Wannan dai al´´amari yazo ne a yayin da manya manyan yan siyasar kasar da kuma masu fada aji suka dukufa wajen ganin an kafa gwamnatin hadaka a tsakanin jam´iyyun kabilun kasar.

Bayanai dai sun nunar da cewa a yanzu haka Faraministan kasar wato Ibrahim Al Jafari na fuskantar matsin lamba na sauka daga mukamin sa don bayar da damar mika sunan mutumin da zai gaje shi, ko hakan ya bayar da damar kafa gwamnatin hadakar.