1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An danganta Rasha da faduwar jirgin MH17

Abdullahi Tanko Bala
November 14, 2019

Masu bincike a kasar Holland sun ce sun nadi wata tattaunawar wayar tarho wadda ta tabbatar da alakar gwamnatin Rasha da harbo jirgin MH17 a sararin samaniyar Ukraine a 2014

https://p.dw.com/p/3T4Z8
Flug MH17
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Wani bincike da hukumomin Holland suka jagoranta ya danganta gwamnatin Rasha da kungiyar 'yan tawayen da aka dorawa alhakin harbo jirgin Malaysia MH17 a sararin samaniyar Ukraine a shekarar 2014.

Bayanani na wasu tattaunawar wayar tarho da aka nada wanda kwamitin binciken ya fitar a wannan Alhamis sun ce an jiwo wasu manyan jami'an gwamnatin Rasha suna tattaunawa da shugabannin kungiyar 'yan tawayen Jamhuriyar al'umma ta Donetsk wadanda suka harbo jirgin da ya hallaka dukkan fasinjoji 298 da kuma ma'aikatan jirgin.

Girkin wanda dan kasar Rasha ne kuma ministan tsaro na Jamhuriyar Donetsk da ya ayyana cin gashin kai yana daya daga cikin mutane hudu da masu binciken suka ce suna da hannu a harbo jirgin.