1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An daure mai cin mutuncin annabi Muhammad

Mouhamadou Awal Balarabe
September 17, 2020

Wata kotu a Bangaladash ta yanke wa wani mabiyin addinin Hindu hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai saboda cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da ya yi a shafinsa na Facebook.

https://p.dw.com/p/3icZO
Bangladesch Oberstes Gericht in Dhaka
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A.M. Ahad

Babban mai gabatar da kara na Dacca babban birnin kasar Bangaladash ya bayyana cewa kotu ta yi amfani da  dokar intanet da aka amince da ita a shekarar 2018 wajen daure Hindu da ya ci mutuncin annabi Muhammad (SAW).  Ita dai kasar Bangaladash wacce galibi al'ummarta Musulmi 'yan Sunni ne, ba ta da addini a hukumance, amma kuma sukar addinin Islama haramun ne a wannan kasa mai jama'a miliyan 168.

An saba samun mummunar zanga-zanga a kasar ta Bangaladash bayan sakonnin sabo da ake watsawa a kafofin sada zumunta na zamani. Ko da a  watan Oktoban da ya gabata, sai dai mutane hudu suka mutu kuma kusan 50 suka ji rauni, a lokacin da wata zanga-zangar da Musulmi suka gudanar domin neman kotu ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi mai bin addinin Hindu da ake zargi da  zagin Annabi Muhammad (SAW) a Facebook.