1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Interpol ta shiga cikin binciken FIFA

Mohammad Nasiru AwalJune 3, 2015

Hukumar 'yan sandar duniya ta Interpol ta sanya sunayen tsaffin jami'an FIFA a jerin wadanda ake binciken yin almundahana kansu.

https://p.dw.com/p/1FbPh
Joseph Blatter
Hoto: Reuters/A. Wiegmann

A dangane da badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol ta sanya sunayen tsoffin jami'an FIFA a jerin wadanda ake gudanar da bikcke kansu. Amirka ce ta gabatar da bukatar sanya sunayen mutanen su shida da suka hada da Jack Warner daga Trinidad and Tobago, da Nicolas Leoz daga Paraguay, da kuma wasu shugabannin kamfanoni hudu daga kudancin Amirka. Ana zarginsu da aikata manyan laifuka da cin hanci da rashawa. Binciken cin hancin da aka kaddamar a kasashen Amirka da Switzerland an mayar da hankali kan zargin cewa an raba na goro lokacin ba da cancantar karbar bakoncin gasar kwallon kafa. A dangane da badakalar cin hancin, a ranar Talata ba zato ba tsammani shugabanin FIFA Joseph Blatter ya ba da sanarwar yin murabus.