1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara cafke almajirai a jihar Kano

March 12, 2014

Dokar haramta bara da majalisar dokokin jihar Kano a Tarayyar Najeriya ta kaddamar ta fara aiki, inda hukumomi a jihar suka ayyana fara kame almajiran da suka ki daina barar.

https://p.dw.com/p/1BOjP
Hoto: DW/T. Mösch

Tun daga Larabannan (12.03.2014) ne aka fara kame almajiran na jihar Kanon ta hanyar kame su a duk sanda a kayi arba dasu. Kafin fara aiwatar da wannan doka dai sai da hukumomin jihar suka samar da jari ga wasu almajirai tare da basu kayan gudanar da sana'oi ga wadanda basu da karfin gudanar da sana'ar kuma mahukuntan sunce an samar musu da albashin naira dubu goma kowannesu. Dokar hana bara wacce ta samar da hukunci mai tsauri ga duk almajirin da yayi kunnen uwar shegu da ita, ta fara aiki ka'in da na'in, duk da cewar dakarun da zasu fara aiwatar da wannan kame basu fantsama zuwa wasu yankunan jihar ba an wayi gari da karancin almajirai a hanyoyi sabanin yadda yake kafin fara aiwatar da wannan doka.

Nigeria Koranschule Schüler
Almajirai da ake kokarin koyarwa ta hanyar zamaniHoto: DW

Almajiran sun fito a wasu tituna

A wasu titunan an sami fitowar almajirai wadanda suka fito domin neman abin kaiwa bakin salati kamar yadda wani almajiri mai suna Baba Nura dake barar a kan titin zuwa Jami'ar Bayero ta Kano ya bayyana. Harabar hukumar Hisbah nan ne ake rarraba kudade da kayan sana'oi ga almajiran da aka haramtawa yin bara har ma wani gurgu mai suna Bashir ya bayyana irin abubuwan da ya samu. Sai dai kuma wasu daga cikin nakasassun da suka yi tunga a bakin harabar sun ce ko karfanfana basu gani ba harma wani dattijo ke cewar matukar aka tafi a haka babu abin da zai hana shi daukar sanda ya cigaba da bara.

Almajiran dake Kano na da yawa

Kasancewar a kwai dimbin almajirai da suke gararambar neman maula ta Sidi maula ta Balarabe a jihar Kano, ya sanya kungiyar nakasassu a jihar ke ganin cewar tallafin da ake bayarwa yayi kadan matuka, dan haka bai kyautu ayi gaggawar fara kamen ba.

Emirs-Palast in Kano
Fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado BayeroHoto: Tanja Suttor-Ba

Malam Abba Sa'idu Sufi shine babban daraktan hukumar Hisbah na jihar kano hukumar da aka dorawa alhakin aiwatar da wannan kame yayi Karin haske a kan wannan aiki da suka fara. Sai dai duk da wannan matakai da ake dauka a wasu wuraren ana samun almajirai suna yin sana'ar tasu ta bara wacce ga alama ke zaman ta yaushe gamo.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Lateefa Mustafa Ja'afar