An fara kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na Zaɓen Mali
August 11, 2013Sama da mutane miliyan shida ne waɗanda suka cancanci yin zaɓen ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen wanda ke cike da mahimmanci ga ƙasar da ta yi fama da rikicin siyasa da kuma yaƙi bayan juyin mulki da sojoji suka yi a shekarun 2011.
Manyan ƙalubale da ke a gaban duk wanda za a zaɓa,sune yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa, da rashin tsaro a yankin arewacin ƙasar da kuma zaman kashe wonda na jama'a galibi matasa. Souleimane Drabo shi ne editan wata mujalla ta ƙasar da ake kira da sunnan Essor.
Ya ce : ''Abin da ake jira kana kuma ake tsamani shi ne mutumin da za a zaɓa ya kasance ya samu cikakkiyar dama ta gudanar da shugabanci fiye da wanda shugabannin da suka shuɗe suka samu''. A zagaye na farko dai na zaɓen Ibrahim Boubacar Keita ya samu kishi 40 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa yayinda Soumaila Cisse ke da ƙasa ga kishi 20.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi