1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kada kuri'u a zaben shugaban kasar Aljeriya

April 17, 2014

'Yan kasar Algeriya da yawan su ya kai Milian 23 na kada kuri'a a zaben shugaban kasar dake gudana a wannan kasa

https://p.dw.com/p/1Bjvg
Hoto: AP

A wannan Alhamis din ce (17.04.2014) 'yan ta kasar Aljeriya ke kada kuri'un su a zaben shugaban kasar, wanda tuni ake ganin cewa shugaban mai ci yanzu Abdelaziz Bouteflika ne zai lashe, a gaban yan adawar dake da rabuwar kawunansu, duk kuwa da cewa yana fama da rashin lafiya.

A jiya Laraba ne dai, aka kawo karshen yakin neman zabe a kasar ta Aljeriya amma ba tare da shugaba Abdelaziz Bouteflika ya halarci ko da daya daga cikin tarurukan gangamin da aka gudanar a kasar ba, inda ya bar masu bashi shawara, da sauran mukarraban sa, suka jagoranci komai na yakin neman zaben a madadin sa.

Jami'an tsaro na yan sanda, da na jandarmomi fiye da dubu 260 ne aka watsa a sassa daban-daban na kasar, inda kusan mutane miliyan 23 zasu zabi daya daga cikin yan takara shidda a wannan zabe, yayin da ake da runfunan zabe a kalla dubu 50 a fadin wannan kasar.

A shekarar da ta gabata ce dai ta 2013 shugaban kasar ta Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya kwanta a wani asibitin kasar Faransa, wanda tun bayan haka ya rage bayyana ta kafofin yada labaran kasar, abun da masu hamayya da shi ke ganin akwai shakku sosai wajan iya tafiyar da mulkin nasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu