1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara nuna damu kan rikicin Nasarawa

Usman ShehuSeptember 19, 2013

Kungiyoyin farar hula sun fara damuwa kan rikicin kabilancin jihar Nasarawa, inda aka hallaka jama'a da dama

https://p.dw.com/p/19krF
epa03141460 Nigerian youths set up burning barricades and confront the police for their inability to prevent a bomb blast at St.Finbarr's parish church in Jos, Nigeria, 11 March 2012. Reports state at least three people were killed during a suspected suicide car bombing at a Catholic church in the central Nigerian city of Jos. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Wani rikicin da yafaru a JosHoto: picture-alliance/dpa

Munin da rikicin kabilanci na jihar Nasarawa ke yi, ya sanya shi zama wanda ya dauki hankalin kungiyoyin wanzar da zaman lafiya da na kare hakkin jama'a, ricikin da sannu a hankali ke watsuwa zuwa wasu sassan jihar.

Rikicin na jihar Nasarawa da ke ci gaba da daukan sabon salo, wanda na baya-baya nan ya kasance rigima ce tsakanin kabilar Ombaste da na Alago, wanda ya yi dalilin kashe daruruwan mutane, da har zuwa yanzu ba'a san adadinsu ba sai dai kawai kotonce.

Kazancewar rikicin da ma bazuwar sa zuwa wasu sassan jihar, da sanin cewa wannan ne karo na biyu da kabilar ta Ombatse ta irin wannan aika-aika, bayan da suka kashe jami'an tsaro fiye da 100 a watan Yulin da ya gabata. Ya sanya nuna damuwa a game da yadda gwamnati ke saku-saku da lamarin. Wannan ya sanya kungiyoyi masu zaman kansu da ke fafutukar wanzar da zaman lafiya da ma kare hakkin jama'a, nuna damuwa da hatsarin da ke tattare da hakan. Malam Dantata Mahmoud na kungiyar masu wanzar da zaman lafiya da tsaro ta Najeriyar, ya bayyana abin da suka hango suke kwarmato a kan batun.

epa03693596 Nigerian relatives of the slain policemen react next to ambulances carrying the bodies to a mortuary in Lafia, Nigeria, 09 May 2013. At least 28 policemen were killed in central Nigeria by an ethnic militia, an official said late 08 May. The clash occurred on 07 May 2013 in Lakwio, near Lafia, the capital of Nasarawa State, said Alhaji Sani Mairiga, the state governor's spokesman. Members of the tribal group Ombatse, meaning 'the time has come' in the Eggon language, reportedly ambushed the police as they approached the village, Police Commissioner Abayomi Akinrimale was quoted as saying by local media. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Inda rikici ya barke a NasarawaHoto: picture-alliance/dpa

"Abin da ke faruwa a jihar Nasarawa ya hada da siyasa da kuma rashin kunya, don haka akwai babban hatsari, mutanen da bai kamata a same su da makamai ba suna da su, idan kuwa mutum na da makami to in dan sanda ko soja ya zo, ina batun tsoro? Ai dama makaman ya sa ake jin tsoronsa, don haka duk wanda ya ce ba hatsari to lallai baya ganin gaba''

Ko da ya ke tuni gwamnatin Najeriya ta aika da jami'an tsaro zuwa yankin domin maido da kwanciyar hankali, sai dai munin irin barnar da aka bari ta faru, inda aka bayyana cewa fiye da mutane hamsin ne aka kashe, kuma wasu dubu bakwai suka rasa mahalansu. Ya sanya yan majalisar dokokin Najeriya da suka fito daga yankin bayyana cewa dole ne fa a sake lale. Sanata Abdullahi Adamu tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne, kuma na cikin wadanda suka bayyana damuwarsu a kan wannan batu.

Autor: Ubale Musa (Korr DW).in Abuja, Nigeria Below are  the pictures of the arrival of the security meeting  PIC FROM LEFT: CHIEF OF DEFENCE STAFF, ADMIRAL OLA IBRAHIM; CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA AND  CHIEF OF DEFENCE INTELLIGENCE, MAJOR-GEN. SANI AUDU ARRIVING FOR A MEETING AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON THURSDAY (4/3/13)
Hafsoshin tsaron NajeriyaHoto: DW

"Ni ina ganin hukuma ba ta yi abin da ya kamata ta yi ba, hukuma ba ta nuna rai yana da daraja a Najeriya ba , hukuma bata dauki hakkin tabbatar da wanda ya yi laifi an hukunta shi ba. Abin nan na faruwa a jihar gwamnan yana mulkin jiha, amma gwamna ai yan sanda ba karkashin ikonsa suke ba, soja ba na shi ba ne ba, yan sandan ciki ba na shi ba ne, sai an ba shi umurni. Kuma an san masu wannan laifin, ana kalonsu ba a ce masu komai ba. Don haka ba abin da ya fi a nuna cewa akwai hukuma a kasar nan, wanda duk ya yi ba dai dai ba a yi ma shi, amma ba a yi wannan ba, kuma da gangan ne''

Zargin saku sakun da ake yi wa gwamnati a kan wannan lamari da ya jefa jihar Nasarwan cikin mumunan hali, ya sanya tambayar shin me gwamnatin ke yi ne, ta bari wannan rikici ya kara kazancewa? Mr Labaran Maku shi ne ministan yada labarun Najeriyar, kuma mai sa ido a kan ma'aikatar kula da harkokin tsaron a yanzu.

Labaran Maku, nigerianischer Informations- und Kommunikationsminister, bei einer Pressekonferenz in Abuja. Copyright: DW/Thomas Mösch
Labaran Maku, ministan yada labaraiHoto: DW/Thomas Moesch

"Mun yi iyakara kokarinmu, mun tabbatar da cewa ana samu zaman lafiya a jihar Nasarawa, ni dan jihar Nasarawa ne. Tun da aka fara wadanan rigingimu na kira taro na shugabanni da yan jihjar Nasarawa, har sau ukum kuma mun sa hannu a rubuce hanyoyin da muke tunanin za'a samu zaman lafiya, kuma mun mikawa shi mai girma gwamnan jihar Nasarawa. Domin muna ganin in mun hada kai mun yi aiki tare jiharmu za ta samu ci gaba''

Najeriya dai kasa ce da ke shan fama da rigingimun da ake danganta su da kabilanci ko addini a lulube, amma kuma masharhanta kan dangata su da cewa na siyasa ne. Saboda kokuwar iko, madafana ikon da akan yi tambayar cewa, shin wa za'a yi wa mulkin ne, idan har babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Usman Shehu Usman