1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara samun ci gaba a harkokin tsaro a yankin Darfur na Sudan

December 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvGI

Shugaban tawagar musanman ta kungiyyar hadin kann kasashen Afrika, wato Au a yankin darfur na kasar sudan, Baba Gana Kingibe yace an samu ci gaba ta fuskar tsaro da zaman lafiya a yankin.

An samu cimma wannan matakin ne kuwa a cewar Baba gana bisa irin aiyukan da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyyar keyi a yankin.

A hannu daya kuma da shiga tsakanin da kungiyyar keyi a tsakanin kungiyoyin yan tawaye da kuma bangaren gwamnati.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Baba Gaba ya fadi hakan ne bayan wata ziyarar gani da ido da tawagar da yakwa shugaban ci ta kai izuwa yankin .

Duk da wannan ci gaba da aka fara samu, a yankin na Darfur , Ambasador Baba Gana ya shaidar da cewa akwai bukatar tabbatar da tsaro da oda a yankin kafin fara dawo da yan gudun hijira izuwa guraren su.