1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara samun masalaha game da rikicin makaman nukiliyar Iran---

Jamilu SaniOctober 13, 2004

Amurka ta ce zata sakawa Iran matukar dai zata dakara da shirinta na kera makaman nukiliya----

https://p.dw.com/p/Bvfb
Hoto: AP

Mukadashin sakataren harkokin wajen Amurka Richard Armitage ya fada a yau laraba cewar koda a baya Amurka ta bukaci a kasar Iran data yi cikaken bayani a kann shirinta na kera makaman nukiliya,to amman kuma halin yanzu Amurka ta bulo da wasu hanyoyi na masalaha ta sulhu maikon kira a gufanar da ita gaban kwamitin sulhu na majalisar dikin duniya don a kakaba mata takunkumin tattalin arziki,tun bayan data gaza yin cikaken bayani kann shirinta na kera makaman nukiliya.

Jami’an diplomaciya na kasahen duniya sun baiyana cewar tun a ranar litinin din data gabata cewar a halin yanzu Amurka ta fara tunani kann shawarar da kasahen turia suka gabatar mata na cewar ta yiwa Iran kyayawar sakaya matukar dai ta amince ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya.

Cikin hirar da jami’an diplomaciya na kasahen duniya suka yi da kungiyar yan jaridu ta kasahen duniya a Vienna jiya talata,sun baiyana cewar manyan jami’an kungiyar hadin kann turia masu shiga tsakani,zasu tashi zuwa birnin washington cikin wanan makon don tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Amurka kann yadda za’a samar da masalaha ta sulhu tsakanin Iran da Amurka.

Tuni aka fara tattaunawa tsakanin Amurka da kasahen turia,a kann yadda za’a shawo kann rikicin makaman nukiliyar Iran.

Fiye da shekara daya ke nan a yayin tarukan hukumar makamashin nukiliya ta majalisar dikin duniya Amurka keta faman yin kira a gurfanar da kasar Iran gaban kwamitin sulhu na majlisar dikin duniya saboda ta ki amincewa ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya wanda kuma yin hakan ya sabawa tsarin dokoki na kasa da kasa.

Bisa tsarin dokoki na kasahen duniya ba’a haramtawa Iran sarafa makamashinta na uranium ba,to amman kuma an shafe watani kasahen duniya na matsawa kasar ta Iran lamba sai ta dakatar da shirinta na sarafa makamashin nukiliya.

Kasar dai ta Iran ta ce tana amfani da fusaharta ta makamashin nukiliya ne wajen samar da hasken wutar lantarki amman ba ke makaman nukiliya ba kamar dai yadda wasu kasahe na duniya ke yi mata irin wanan zargi.

Koda yake cikin watan Octoban shekarar data gabata Iran ta cimma yarjejeniya da kasahen Birtania,Jamus da Faransa dangane da dakatar da shirinta na sarafa makamashin nukiliya na wucin gadi don ta baiwa masu bicikin makamai na hukumar IAEA gudanar da bincike a yankunan da ake zargin tana kera makaman nukiliya,to amman kuma daga baya Iran ta ce ta dakatar da dukanin wani hadin kai da take bayarwa a fuskar binciken makaman nukiliyar da ake zargin tana kerawa.