1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron kasashen G20 a China

Suleiman BabayoSeptember 4, 2016

An fara taron manyan kasashen masu karfin tattalin arziki a China. Kungiyar G20 ta hada kasashe mafi karfin tattalin arziki na duniya.

https://p.dw.com/p/1JvYq
China G20 Gipfel in Hangzhou - Hollande & Jinping & Putin & Merkel
Hoto: Reuters/N. Asfouri

A wannan Lahadi aka bude taron shugabannin manyan kasashen duniya da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki na Kungiyar G20 a birnin Hangzhou na kasar China. Kuma neman hanyoyin bunkasa tattaklin arziki na cikin abin da ke kan gaba da za a tattauna yayin zaman taron na kwanaki biyu. Shugabannin kasashen masu karfin tattalin arziki da ke cikin mahalarta taron sun hada da shugaba Barack Obama na Amirka, da shugaba Vladimir Putin na Rasha, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da Firaminista Teresa May na Birtaniya gami da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya.

Shugaba Xi Jinping na China mai masaukin baki ya nemi ganin amfani da wannan dama wajen habaka tattalin arzikin duniya da bunkasa cinikaiya tsakanin kasashe. shugaban ya fadi haka yayin jawabin bude taron.