1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron kolin Kasashen Musulmi a Alkahira

February 6, 2013

Halin da Siriya take ciki na tsaka-mai-wuya na daga cikin al'amuran da zasu dauki hankali a zauren taron kungiyar musulmi ta OIC

https://p.dw.com/p/17YtS
Hoto: Getty Images

Shugabannin kasashen kungiyar musulmin duniya, wato OIC, ranar Laraba sun bude zaman taron kolin su na 12 a Alkahira, babban birnin Masar. Manyan al'amuran da taron yake dubawa sun hada harda yakin basasa a Siriya da kuma yakin da kasashen taron dangi suke yi kan kungiyoyi na kishin Islama a kasar MaliMinistocin

Lokacin da guguwar neman sauyi ta fara kaɗawa a Siriya, masu lura da al'amuran sun yi hasashen cewar gwamnatin shugaban Bashar Al-Assad za ta fadi cikin gaggawa, kamar sauran ƙasashen larabawa da suka fuskancin wannan canji. To saidai kusan shekaru biyu bayan ɓarkewar rikicin Siriya, har yanzu shugaba Assad na cigaba da nuna turjiya mai tsanani.

Alƙalluman da Majalisar Dinkin Duniya ta wallaffa sun haƙiƙance cewa a tsukin kusan shekaru biyu da aka share a na gawbaza faɗa tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da 'yan tawaye, mutane fiye da dubu 60 suka rasa rayuka, sannan a ƙalla miliyan biyu suka ƙauracewa gidajensu, wasu a cikin ƙasar, a yayin da wasu kuma suka tsallaka ƙasashen ƙetare. Kasashen Turkiyya, Jordan Lebanon da Iraki su kaɗai sun ƙunshi 'yan gudun hijirar daga Siriya fiye da dubu 600.Kazalika, Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira ta tabbatar da cewa a safiya ta Allah akwai mutane dubu biyu zuwa dubu ukku dake ƙauracewa ƙasar Siriya.

Syrien Präsident Bashar al-Assad im Staatsfernsehen
Shugaban Siriya Bashar Al-ASsadHoto: DSK/AFP/GettyImages

Masu nazarin rikicin Siriya sun hango tarnaƙi guda biyu wanda ke kawo cikas wajen gano bakin zaren warware wannan zubar da jini.

Na farko dai shine kiki-kaka da ake fuskanta a komitin Sulhu an Majalisar Dinkin Duniya, wajen ɗaukar matakin bai ɗaya ga hukumomin Damscus sai kuma tallafin kuɗaɗe da makamai da ɓangarorin biyu ke samu daga ƙasashen ƙetare kamar yadda Robert Schütte na ƙungiyar yaki da aikata kisankiyasu wato " Genocide Alert" ya yi baiyani:

" A ganina halin da ake ciki Siriya misali ne kyakyawa game da hatsarin dake tattare da saida makamai a yankunan da ke fama da rikici.Domin da zaran wannan makamai suka shiga babu mai masaniya ghame da irin amfanin da za a yi da su".

A cikin wannan rikicin da ya ƙi ya ci cinyewa a Siriya,a na zargin Iran da taimakawa shugaba Bashar Al-Assad da makamai a yayin da 'yan tawaye ke samun tallafi daga Saudi Arabiya da kuma Qatar. Dalili da sasaucain ga dokokin dake tattare da cinikayar makamai, 'yan tawaye AQMI da masu tasatsauran kishin addinin Islama suka yi amfani da makaman tsofan shugaban ƙasar Libiya marigayi Mohamar Khadafi.

Mali Armee Ansongo 29.01.2013
Farin cikin 'yanto Mali daga hannun kungiyoyin IslamaHoto: Kambou Sia/AFP/Getty Images

A irin wannan hali na rashin tabbas, ya zama wajibi ga ƙasashen da ke saiyar da makamai sun ƙara sa ido da kuma tsaurara dokokin cinakin makamai inji Rolf Mützenich kakakin harkokin ƙetare na jam'iyar SPD mai adawa a Jamus:

"Ya kamata mu matsa ƙaimi wajen sa ido ga ƙasashen da muke saidawa makamai, sannan mungin daya dokoki masu tsarii ta yada wannan makamai ba za su shiga ba cikin miyagun hannuwa.Ta haka ne kawai za mu iya riga kafi ga abkuwar ta'asar da ake yi da makaman da mu ke ke sayarwa wasu ƙasashe".

Ta ko wane hali za'a cewa gamayar ƙasa da ƙasa ta yi sake game da rikicin Siriya, wanda a yanzu kusan ya gagari kundila, ta la'akari da yadda ƙananan makamai su ka yadu a cikin ƙasar wajen daidai kunmutane.Ko da an yi nasara warware wannan rikicin watan wata rana za a ci karo da illoli masu yawa saboda wannan huja inji Professa Claus Kreß na cibiyar nazarin dokokin yaki da ta'adanci a jami'ar birnin Cologne da ke Tarayya Jamus.

Mawallafi: Anne Allmeling/Yahouza Sadissou
Edita: Umaru Aliyu