1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron 'yan darikar Orthodox na tarihi a kasar Girika

Mohammad Nasiru AwalJune 20, 2016

Taron da ke zama irinsa na farko cikin sama da shekaru dubu daya, na da nufin samun hadin kan cocin Orthodox a duniya.

https://p.dw.com/p/1JAGd
Die Führer der christlich-orthodoxen Kirchen
Shugabannin cocin Orthodox da ke halartar taronHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Hawkey

Shugabannin mabiya darikar cocin Orthodox na duniya sun hallara a karon farko cikin shekaru kusan 1000 don gudanar da wani taro na tarihi da zumar inganta hadin kai tsakaninsu. Sai dai rashin halartar wasu cocin 'yan Orthodox ciki har da na Rasha na barazanar rage armashin taron. A jawabinsa ga mahalarta taron, shugaban cocin Bartholomew na Daya na Constantinople ya mika godiyarsa yana cewa.

"A cikin farin ciki ina yi muku maraba da kuka kasance tare da mu a wannan taron mai cike da tarihi na 'yan Orthodox. Kamar yadda kuka sani mun kwashe shekaru gommai muna shirye-shirye tare da kaunar gudanar da wannan taro. Taimako da goyon baya da kuma addu'o'in da kuka raka mu da su a tsukin wadannan shekarun sun kara mana kwarin guiwa."

Shugaban taron ya kuma nuna takaicinsa yadda ake samun rarrabuwar kai tsakanin cocin na Orthodox a duniya, inda ya yi fata taron zai gano bakin zaren wannan matsala.