1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara tattauna rikicin Siriya a Geneva

Charlotte Chelsom-PillJanuary 25, 2014

A karon farko wakilan gwamnatin Siriya da na 'yan adawa sun yi ganawa ta gaba da gaba a ƙarƙashin jagorancinLakhdar Brahimi babban mai shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/1AxE3
Syrien Konferenz in Montreux Lakhdar Brahimi & Ban Ki-Moon 22.01.2014
Hoto: Philippe Desmazes/AFP/Getty Images

Ɓangarorin biyu waɗanda suka shiga zauren taron MDD na Geneva a ƙofofi daban-daban, sun kwashe wani ɗan takaitaccen lokaci suna sauraron jawabin Lakdar Brahimi a kan yunƙurin neman sulhu a rikicin na Siriya ba tare da yi wa juna magana ba.

Yanzu haka dai sassan biyu na can sun shiga tattaunawa batuttuwa mafi mahimmanci kamar yadda wani mai sulhuntawa na 'yan adawa Anas Albade ya sanar. Ya ce : '' Maganar dakatar da buɗe wuta da kuma kai kayan agaji a garin Homs na daga cikin batutuwan da muke ƙoƙarin ganin an samu daidaituwa a kansu kafin a kai ga maganar fursunonin siyasa da waɗanda aka sace.''

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba