1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaɓen 'yan majalisa a Amirka

November 4, 2014

Zaɓen na 'yan majalisar wakilai da na dattawa na iya zame wa shugaba Obama na Amirka ƙadangaren bakin-tulu saboda zai iya haddasa masa cikas a harkokin mulki.

https://p.dw.com/p/1DgXl
Hoto: Reuters/C. Keane

An fara kaɗa ƙuri'u a kasar Amirka da nufin zaɓen 'yan majalisan wakilai na tarayya da na dattawa da ma na gwamnoni a wasu jihohin ƙasar. Jihohi shida ne suka fara buɗe runfunan zaɓen sakamakon banbancin lokacin da ke tsakanin sassa ƙasar ta Amirka, daga cikinsu kuwa har da Connecticut da New Jersey da New York da indiana da kuma Kentucky. Mutane miliyan 200 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a domin sabinta ɗaukacin kujerun majalisar wakilai, da kujerun dattawa 36 daga cikin 100, da kuma na gwamnoni 36.

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta nunar da cewar jam'iyyar Republican za ta samun rinjaye a majalisar wakilai. Sannan kuma jam'iyyar Democrat ta su shugaban Barack Obama za ta iya shan kaye a majalisar dattawa. Idan ko hasashen ya tabbata, to dai Obama zai fuskanci ƙalubale wajen gudanar da harkokin mulki saboda turjiya da zai fuskanta da 'yan Republican da za su sami rinjaye a majalisun biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane