1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaben raba gardama a Thailand

August 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuDf

A yaune yan kasar Thailand ke kada kuri´r raba gardama kann sabon kundin tsarin mulki da sojin kasar suka tsara shi.Kusan yan kasar miliyan 45 ne ake sa ran zasu shiga wannan zabe na yau. Rahotanni dai sun rawaito wasu masana na cewa wannan zabe koma baya ne a game da tafarkin mulkin dimokradiyya a kasar.A waje daya kuma, wasu na da ra´ayin cewa amincewa da wannan kundi ka iya kawo karshen mulkin soji a kasar.Bayanai dai sun nunar da cewa, matukar yan kasar suka amince da wannan kundi, to ala tilas sojin kasar dake rike da mulki yanzu zasu kira zaben gama gari a watan disambar wannan shekara.A watan satumbar bara ne sojin suka kifar da mulkin faraminista Thaksin Shinawatra, bisa zargi da suka yi masa na cin hanci da rashawa. Hakan dai ya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin yan kasar, wanda hakan ya bawa sojin damar rike madafun ikon kasar har na tsawon watanni 11.