1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaben yan Majalisu a kasar Iraki.

April 30, 2014

'Yan kasar Iraki fiye da miliyan 20 ne za su kada kuri'un su a zaben 'yan majalisun dokokin kasar dake gudana a wannan Laraba (30.04.2014).

https://p.dw.com/p/1Br8l
Irak Wahlen April 2014
Hoto: SABAH ARAR/AFP/Getty Images

Wannan dai shi ne karo na farko da kasar ta Iraki ke shirya irin wannan zabe, tun bayan janyewar dakarun Amirka daga kasar, inda kafin karfe shidda na yammacin yau a agogon kasar za rufe rumfuna. 'Yan kasar za su zabi wakilai 328 daga cikin 'yan takara fiye da 9000, duk kuwa da cewa kasar na fama da matsalolin tashe-tashen hankula da hare-hare, wadanda kawo yanzu suka haddasa rasuwar mutane fiye da dubu uku, tun daga farkon shekara.

Ana ganin cewa, Firaministan kasar Nouri Al-Maliki da ke neman wani wa'adi na uku, zai taka rawar gani cikin wannan zabe, inda ma yake ganin zai yi nasara.

Manyan kaluba da ke addabar kasar ta Iraki dai sun hada da matsalolin yawan marassa ayyukan yi, da cin hanci sannan batun sake dawo da ingantattun ma'aikatun gwamnati a wannan kasar.

Sai dai an gudanar da yakin neman zaben bisa alkawura na samar da tsaro, a cikin kasar da a kalla mutane 25 ne ke mutuwa a ko wace rana, sakamakon tashin hankali tun daga watan Janairu da ya gabata. Inda a 'yan kwanakin baya-bayan nan ma aka kashe a kalla mutane fiye da 90, abun da ake ganin zai iya haifar da karancin masu fita domin zaben.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman