1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cire kan wani a Faransa

Yusuf BalaJune 26, 2015

Tun dai a safiyar Juma'an nan shugaban Faransa Francois Holland ya ce wannan hari na da alaka da ta'addanci .

https://p.dw.com/p/1Fo1Q
Frankreich Anschlag bei Grenoble
Hoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Baya ga sauran kasashen duniya da suka hadar da Jamus, firaministan kasar Spain Mariano Rajoy ya yi Allah wadai da harin ranar Juma'an nan, harin da aka kai wata masana'antar albarkatun gas a Faransa. Ya ce duniyar demokradiya ba za ta lamunci wannan aiki ba da ke zama na rashin imani.

Firaminista Rajoy ya ce da kakkausan harshe ya yi Allah wadai da harin da aka kai birnin Lyon . Ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, ayyuka na rashin imani na bukatar hadin kan kasashe masu martaba demokradiya.

Tun dai a safiyar Juma'n nan shugaban Faransa Francois Holland ya ce wannan hari na da alaka da ta'addanci an kuma samu damar cafke wanda ake zargi .


Ya ce "Harin, hari ne na ta'addanci tun da an samu gawar wanda aka halaka an datse masa kai, sannan an ajiye wasu bayanai cikin harshen larabci a bakin kofa, yanzu akwai mutum guda da ya rasu wasu kuma sun jikkata".

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve ya je wurin tare da mai gabatar da kara an kuma jibge jami'an tsaro.