1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farautar wadanda suka kakkabo jirgin saman Malaysiya

Ramatu Garba Baba
June 19, 2019

Igor Girkin jagoran 'yan awaren Ukraine da ake nema ruwa a jallo, ya musanta zargin hannu a kakkabo jirgin saman kasar Malaysiya MH17 da ya halaka mutum 298 a shekarar 2014.

https://p.dw.com/p/3KinX
Flug MH17
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Jagoran 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha ya isar da sakonsa ne daga Rasha. Kwararru daga kasashen Holland da Australiya da Beljium da Ukraine da kuma Malaysiyaa, sun gano cewa, mutanen sun yi niyyar kakkabo wani jirgin yakin soja ne a sararin samaniyan yankin da Rasha da Ukraine ke jayayya a kai amma bisa kuskure,  kaddara ta fada kan jirgin na Malaysia.

Jirgin MH17 kirar Boeing 777 da ke kan hanyarsa ta zuwa Malaysiya bayan da ya taso daga birnin Amsterdam ya fadi inda duk wadanda suke cikinsa suka rasa rayukansu. Bincike dai ya gano wasu mutane hudu da hannu a kakkabo jirgin, uku 'yan asalin kasar Rasha ne yayin da guda ya kasance dan kasar Ukraine.