1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da 'yan sanda 29 bisa kyamar baki

Mohammad Nasiru Awal SB
September 16, 2020

A Jamus an dakatar da 'yan sanda 29 daga aiki, ana kuma gudanar da bincike kansu bisa zargin musayar wasu bayanan farfaganda ta masu tsananin kyamar baki.

https://p.dw.com/p/3iaEa
Deutschland Wuppertal | Razzia gegen Clankriminalität
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kusch

Hukumar 'yan sanda da ke a jihar North Rhine Westfalia, mafi yawan al'umma a tarayyar Jamus, sun fara gudanar da bincike kan wasu jami'an 'yan sanda 29 da ake zargi da musayar wasu takardun farfaganda ta masu tsattsuran ra'ayin kyamar baki a yanar gizo.

Ministan harkokin cikin gidan jihar da ke a yammacin Jamus, Herbert Reul ya ce an dakatar da 'yan sandan daga aiki. Ya ce a dandalin sada zumunta na intanet din 'yan sandan da ake zargin sun yada hotuna na Hitler da alamomin masu kyamar baki da wasu zane-zane da ke nuni da yadda za a iya kone 'yan gudun hijira a irin sansanonin na ihunka a banza.

Ministan cikin gidan na jihar ta North Rhine Westfalia, ya bayyana halayyar 'yan sandan da wani abin kunya ga 'yan sanda.