An gaza cin kyautar Mo Ibrahim
October 14, 2013Talla
Hukumar wacce aka kafa a shekarun 2006 na ba da kyautar ga tsofin shugabannin da gwamnatocin Afirka, wanda suka taka rawar ganin wajen samin ci gaba da kuma ɗorewar demokraɗiyya a cikin ƙasahensu.
Da yake magana shugaban kwamitin Ahmed Salim Ahmed tsohon sakataran ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka a lokacin OUA, kana tsohon shugaban gwamnatin Tanzaniya. Ya ce bayan dogon nazarin kwamitin bai ga wanda ya cancanci samin kyautar ba, ta dala miliyan biyar. Daman dai a kwanan baya, Mo Ibrahim ɗin wani attajirin ɗan kasuwa na ƙasar Sudan wanda ake yin kyautar da sunansa,ya yi kakausar suka ga salon mulki na shugabannin Afirka.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal