1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka wanda ya kai hari Jamus

December 23, 2016

'Yan sandan Italiya sun tabbatar da harbe mutumin da ya kai hari birnin Berlin fadar gwamnatin kasar Jamus cikin wannan makon.

https://p.dw.com/p/2Un7N
Italien Terrorverdächtiger Anis Amri in Mailand erschossen
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Bennati/B&V

Mahukuntan Italiya sun tabbatar da hallaka mutumin da ake nema bisa zargi da hannu wajen hari a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Anis Amri dan asalin kasar Tunisiya ya rasa ransa lokacin da ya yi musanyen wuta da 'yan sanda a birnin Milan na Italiya, wadanda suka tsare shi, sannan suka tambaye shi ya nuna katin shaida, amma maim akon haka sai ya bude wuta.

Dan sanda daya ya samu raunika, yayin da daya dan sandan ya samu nasarar kashe matashin da ake nema ruwa a-jallo. Ministan kula da harkokin cikin gida na ItaliyaMarco Minniti ya shaida wa taron manema labarai cewa tuni masu bincike suka tabbatar mutumin da aka harbe Anis Amri ne da ake nema sakamakon harin da aka kai kasar Jamus.

A cewar babban jami'in 'yan sanda na birnin Milan marigayin ya isa kasar ta Italiya ta jirgin kasa daga Faransa.