1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka wani babban sojin kasar Burundi

Suleiman BabayoAugust 2, 2015

Janar Adolphe Nshimirimana babban jami'in leken asiri kuma wanda ake dauka mutum na biyu a gwamnatin kasar ya mutu lokacin da aka harba rokoki biyu cikin motar da yake tafiya

https://p.dw.com/p/1G8d7
Burundi, Wahlkampfveranstaltung der CNDD-FDD
Hoto: DW/K. Tiassou

'Yan bindiga sun kashe daya daga cikin manyan habsoshin sojin kasar Burundi kana na hannun damar Shugaba Pierre Nkurunziza, lokacin da yake tafiya a cikin mota a birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar.

Jami'ai da shaidun gani da ido sun Janar Adolphe Nshimirimana babban jami'in leken asiri kuma wanda ake dauka mutum na biyu a gwamnatin kasar, ya gamu da ajalinsa lokacin da aka harfa rokoki guda biyu cikin motarsa inda nan take ta kama da wuta.

Lamarin na wannan Lahadi ya kara fitowa matsalolin da kasar ta Burundi take ciki tun lokacin da Shugaba Pierre Nkunrunziza ya yi tazarce bayan karewar wa'adin mulkinsa na shekaru 10. Tun lokacin ake nuna tsaron kasar za ta sake iya fadawa cikin yakin basasa.