1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbo wani jirgin saman fasinjan Malaysia a gabashin Ukraine

July 17, 2014

Jirgin saman dauke da mutane 295 ya fadi a wani yanki da ke gabashin kasar Ukaine kuma dukkan mutanen da ke ciki sun rasu.

https://p.dw.com/p/1CejO
Absturzstelle Malaysia Airlines MH-17 Ukraine
Hoto: Reuters

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya ce mai yiwuwa an harbo wani jirgin saman fasinjan kasar Malaysia da ya yi hadari a yankin da ke karkashin 'yan tawaye na gabashin Ukraine. A cikin wata sanarwa da ya wallafa shafinsa na intanet Poroshenko ya ce ba za su iya musanta cewa an harbo jirgin ba ne, amma sun tabbatar cewa mayakan sama na Ukraine ba su harba wani makami sararin samaniya ba. Kamfanin dillancin labarun Rasha Itar-Tass ya rawaito wata majiya a hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Ukraine na cewa dukkan fasinjoji 280 da ma'aikatan jirgi 15 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu. Jagororin 'yan tawaye sun fada wa kamfanonin dillancin labarun Rasha cewa ba su suke da alhakin harbo jirgin saman ba kuma sun dauki alkawarin kyale masu bincike na kasa da kasa shiga yankin don gudanar da bincike. Jirgin saman yana kan hanya daga birnin Amsterdam na kasar Holland zuwa Kuala Lumpur a Malaysia. A farkon watan Maris wani jirgin saman Malaysia dauke da daruruwan mutane ya yi batar damo a kan hanyarsa daga Malaysia zuwa China kuma har yanzu ba a gan shi ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo