1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ja kunnen 'yan siyasan Madagaskar

Usman ShehuAugust 6, 2013

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ɗibarwa shugabannin siyasa a Madagaska, nan da mako biyu da su warware bambance-bambance da ke tsakaninsu

https://p.dw.com/p/19KaW
(FILE) A file photo dated 21 March 2009 shows Madagascar President Andry Rajoelina (C - with sash) walking past military personnel after being sworn in in Antananarivo, Madagascar. An army general in Madagascar declared 17 November that he had suspended the island_s institutions - as millions of people voted on a new constitution. General Noel Rakotonandrasana, ex-minister of the armed forces, told a press conference at a barracks near Antananarivo airport that a military committee had taken power from the interim authority of embattled leader Andry Rajoelina. EPA/SAM TCHE' +++(c) dpa - Bildfunk+++
Andry Nirina Rajoelina shugaban ƙasar MadagaskarHoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ja kunnen dukkan waɗanda ke kawo cikas ga gudanar da zaɓe a ƙasar Madagaska, inda aka basu nan da makwannin biyu da su warware rikicin siyasar ƙasar. Kantomar harkokin ƙetare a ƙungiyar EU Catherine Ashton ce ta bada sanarwar cewa, duniya ba za ta lamunta a ci gaba da hana ruwa gudu don komawar ƙasar mulkin demokradiyya ba. Tun dai bayan juyin mulkin da ya ɗora Andry Rajoelina kan mulki a shekara ta 2009 aka kasa gudanar da zaɓe bisa rarrabuwar kawunan 'yan siyasa. Masu shiga tsakani daga ƙungiyar Tarayyar Afirka sun bada shawar cewa 'yan takara uku da suka hana ruwa gudu, wato shugaba mai ci Andry Rajoelina da Lalao matar Marc Ravalomanana wanda Rajoelina ya karɓi mulki a hannunsa da kuma Didier Ratsiraka da cewa duk su ajiye takaransu ko a samu lafawar al'umura, inda yanzu komai ya dagule wa 'yan siyasan, amma duk 'yan takarn kowa ya yi ƙememe.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita:      Yahouza Sadisou Madobi