1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta baci a kasar Philippines

February 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6o

Shugabar ƙasar Philippines Gloria Macapagal Arroyo ta kafa dokar ta baci a ƙasar bayan da jamián tsaro suka sanar da cewa sun murkushe wani yunkurin juyin mulki da aka shirya mata. Rahotanni sun baiyana cewa a halin da ake ciki an kame manyan jamián soji da dama a dangane da zargin juyin mulkin. Manazarta alámuran yau da kullum na baiyana cewa gwamnatin Gloria Arroyo na ƙara kambama yunƙurin juyin mulki ne domin ta sami goyon bayan jamaá a yayin bikin cika shekaru 20 da hamɓarar da gwamnatin kama karya ta Ferdinand Marcos. Sai dai kuma a hannu guda, gwamnatin ta bada izini ga tsohon shugaban ƙasar Corazon Aquino ya gudanar da taro domin tunawa da ranar juyin juya hali na ƙasar wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali shekaru ashirin da suka gabata. A waje guda kuma da sanyin safiyar yan sanda a birnin Manila sun yi amfani da feshin ruwan zafi domin tarwatsa gungun masu zanga zanga wadanda yawan su ya kai 5000 da suka fito domin nuna adawa da gwamnatin Arroyo.