1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta-baci a Sudan

February 23, 2019

Sakamakon zafin zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar Sudan, Shugaba Omar Hassan al Bashir na kasar ya ayyana kafa dokar ta-bacin shekara guda.

https://p.dw.com/p/3DwvZ
Sudan | Präsident Al-Bashir erklärt Nationalen Notstand
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Shugaba Omar Hassan al Bashir na kasar Sudan, ya ayyana kafa dokar ta-bacin shekara guda a kasar, tare ma da rusa majalisar gudanarwar gwamnatin tarayya da ta kananan gundumomi.

Shugaban wanda ke fama da tsananin matsin lamba na ya sauka daga karagar mulki, ya sanar da hakan ne a jawabin da ya yi ta kafafen yada labaran kasar a jiya Juma'a.

Dan shekaru 75 da ake bayyanawa da mai mulkin kama-karya, ya kuma yi kiran majalisar dokokin kasar da ta dakatar da yi wa kundin mulkin kasar kwaskwarimar da za ta ba shi damar sake neman takara a badi.

A makonnin baya ne aka fara zanga-zangar neman Shugaba al Bashir ya sauka daga mulkin Sudan din, da ya yi shekaru 30 a kai.