1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya dagargaza kasuwar N'Djamena

Salissou BoukariJuly 11, 2015

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da safiyar wannan Asabar din a babbar kasuwar birnin N'Djamena na kasar Chadi, ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1FxAL
Tschad - N'DJAMENA
Hoto: Getty Images/M. Di Lauro

Wani namiji ne dai ya yi shigar mata sanye da hijabi ya tayar da wannan bam a daidai lokacin da wani jami'in tsaro na jandarma ke kokarin bincikensa, ganin irin matakan tsaron da hukumomin kasar suka dauka a wannan kasa. Akalla mutane 15 sun rasu, wadanda suka hada da mata 'yan kasuwa guda tara, da maza biyar da kuma jandarma guda, bayan wadansu da dama da suka jikkata. Shaidun gani da ido sun ce sun ga sassa mutane a yashe, sannan kuma jini ya kwarara sosai a wurin. Jim kadan ne dai jami'an tsaron kasar ta Chadi suka killace kasuwar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da birnin na N'Djamena ke fuskantar irin wannan hari na kunar bakin wake, inda a ranar 15 ga watan Yuni da ta gabata wani harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 38 a makarantar horas da 'yan sanda da kuma ofishin 'yan sanda na babban birnin kasar, harin da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai shi. A baya dai hukumomin kasar ta Chadi sun bada sanarwar hana saka nikab, hijabin nan da ke lullube illahirin jikin mace ta dalilin irin haka.