1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kakkabe cutar Polio a Niger da Masar inji Hukumar kiwan lahia ta Majalisar Dinkin Dunia

February 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9p

Hukumar kiwan lahia, ta Majalisar Dinkin Dunia , ta bada rahoton cewa ta samu nasara murkushe cutar Polio a kasashen Masar da Jamhuriya Niger.

Hakan wata alama ce mai nuna cewar hukumar na kussa da cimma burin ta, na karewa kwata kawata da wannan annoba a doron dunia.

A shekara da ta gabata, inji sanarwar da kungiyar WHO ko kuma OMS, ta hiddo jiya, babu yaro daya, da ya kamu da kwayoyin wannan cuta a kasashen 2.

A game da Niger, an samu yara 9 masu cutar,saidai dukan su, sun samo ta, daga makobciya, Tarayya Nigeria, inji rahoton WHO.

A halin da ake ciki kasashe 4 kadai, ke fama da cutar Polio, da su ka hada da Nigeria, India, Pakistan da Afghanistan.

A lokacin da hukumar OMS, ta fara yakin gama dunia, na kakkabe cutar Polio, a shekara ta 1988 ,kasashe 128 ke fama da cutar.

Saidai duk da nasara da aka samu, za a ci gaba da kokarin ida gamawa da wannan cuta, a ragowar kasashen, da ma Jamhuriya Niger da ke makobtaka da Nigeria inji shugaba sashen yaki da Polio a Majalisar Dinkin Dunia.