1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama hanyar ceto takardun kuɗin Euro

October 19, 2012

Taron ƙolin ƙungiyar EU a Brussels ya amince da ƙa'idojin kafa hukumar sa ido a kan bankunan ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro don ceto wannan kuɗi.

https://p.dw.com/p/16TZF

Manyan shugabannin ƙungiyar sun ce sun yi nasara. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gamsu a kan batun kafa hukumar da za ta sa ido kan bankunan nahiyar Turai, sannan shi ma shugaban Faransa Francois Hollande ya nuna farin ciki kan wannan ci gaba da aka samu dake da nufin ceto takardun kuɗin Euro da ma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashen Turai dake fama da matsalolin kuɗi.

Shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai dake halartar taron ƙolin birnin Brussels sun nuna gamsuwarsu da amincewa da ƙa'idojin kafa hukumar da za ta sanya ido a kan harkokin bankunan da cewa muhimmin mataki ne da ke da nufin ƙarfafa haɗakar kuɗin bai ɗaya na Euro. A lokacin da yake magana bayan amincewa da sharuɗɗan farko na kafa hukumar shugaban Faransa Francois Holland ya ce babban ci-gaba ne aka samu.

"An cimma yarjejeniya mai kyau a kan tsarin lokaci, wadda ta ƙunshi dukkan bankuna. Yarjejeniyar ta nuna aniyyar aiwatar da dukkan tsare tsare da aka sa gaba. Wannan yarjejeniya ce mai kyau."

A yi sara ana duban bakin gatari

Sai dai Firaministan Belgium Elio di Rupo ya yi kashedi da a yi takatsantsan, domin kowane wakili daga wakilai 27 na majalisar ministocin Turai na wakiltar manufa da buƙatar ƙasarsa da kuma ta Turai. Wannan kuwa ya fito fili tun gabanin taron ƙolin inda aka samu rashin jituwa tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Francois Hollande game da kafa hukuma sa idon akan bankunan Turai. Sai dai bayan cimma yarjejeniyar an jiyo Merkel na cewa.

Brüssel EU-Gipfel Gruppenbild
Hoto: AP

"Dukkanmu mutane ne dabam dabam. Amma duk da haka muna gano hanyoyin samun haɗin kai don cimma manufar da aka sa gaba. Kuma kamar yadda kuka gani mun gano bakin zare warware babbar matsalar mu. Wannan shi ne muhimmin abu."

Har yanzu da bambamcin ra'ayi

Sai dai tamkar riga mallam masallaci ne idan aka yi maganar warware matsalar yanzu. Domin akwai batutuwan da ke buƙatar a yi bayani kansu wato ba gaggawar magance su ba, ko wace na da buƙatunta na ɓoye. Alal misali Jamus tana ƙoƙarin ganin an cire wasu bankunanta daga jerin bankunan da masu binciken na Turai za su wa ido. Ita kuwa Faransa tana son dukkan bankuna 6000 na ƙasashen dake amfani da kuɗin Euro su kansance ƙarƙashin sa ido hukumar ta tsakiya. Hakazalika Jamus na fargabar cewa bisa ra'ayin na Faransa, ana iya ɗora wa wata ƙasa nauyin bashin wata ta bayan fage, ƙaƙashin sharuɗɗan wani asusun ceto bankuna na bai ɗaya a Turai.

Duk da haka dai shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ce an buɗe hanyar rage raɗaɗin matsaloli a ƙasashe masu fama da rikicin kuɗi tare da tallafa wa hukumomin kuɗi kai tsaye da kuɗaɗen ceto na Turai.

Brüssel EU-Gipfel Hollande Merkel Barroso
Hoto: Reuters

"Kar ku bari mu manta da dalilin da ya sa muke wannan aiki. Muna samun ci-gaba ga matakan da muke ɗauka na tinkarar rikicin kuɗi, yanzu ya zama wajibi mu rarrabe tsakanin bashin banki da na ƙasa."

A taron da za su yi cikin watan Nuwamba ministocin kuɗi na ƙungiyar ta EU za su tattauna tare da tsara yadda hukumar za ta yi aiki. Sai dai kamata yayi a amince da ƙa'idojin kafin ranar ɗaya ga watan janeru amma ba wai cimma yarjejeniya kansu ba domin za a ɗauki tsawon watanni kafin majalisar Turai ta amincewar ƙarshe ga ƙa'idojin.

Mawallafa: Christoph Hasselbach / Mohammad Nasiru Awa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe