An kama manyan jami'ai a Habasha
November 13, 2018Talla
Manya-manyan kame da ake yi a kasar ta Habasha, na zuwa ne bayan umurnin da Firaminintsa Abiy Ahmed ya bayar na aiwatar da bincike kan wadanda suka aikata ba dai dai ba lokacin gwamnatin da ta gabata.
Wasu ma daga cikin kamen da aka yi sun hada da wadanda ake zargin suna cuzguna wa fursunoni a gidajen yari da azaftar da jama'a da sunan neman bayanai da fyade; sai kuma uwa-uba kisa.
Haka ma daga cikin wadanda ake nema a yanzu, har da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar, wanda ake zargin shi da hannu a yunkurin halaka Firaminista Abiy a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata.