1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala hawan Arafat

November 15, 2010

Aikin Hajji bana ya gudana lami lafiya cikin tsatsaura matakai tsaro

https://p.dw.com/p/Q9ta
Dakin Ka'abaHoto: picture-alliance/dpa

Musulmi kimanin miliyan uku sun hallara a filin Arafat a yau Litinin domin gudanar da ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ibada na Hajji. Hawa dutsen Arafat dai na zama ƙololuwar aikin Hajji a kowace shekara a ranar tara ga watan zulhaji.

Ma'aikatar cikin gidan Saudiya ta ce a bana Musulimi kimanin miliyan 1.7 daga ƙasashen duniya 181 suka shiga daular ta ƙasa mai tsarki domin gudanar da wannan ibada dake zama ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar.

An dai tsaurara matakan tsaro ga aikin na hawan Arafat da yanzu haka aka kammala

 Mohammed Baki wani dan kasar Siriya na daga cikin rukunin jamaar da suka yi aikin hajin.

Yace abin farin ciki ne mafi misali a wannan rana da Allah ya bamu iko aikata wadanan ayyuka na alheri domin samun rahamar Allah da kuma neman gafartarsa. .

Mawallafi : Abdurahaman Hassane

Edita       : Abdullahi Tanko Bala