1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taro kan addinin Islama a birnin Vienna

Mohammad Nasiru AwalNovember 17, 2005

Taron ya mayar da hankali a kan rawar da Islama ke takawa a zamantakewa tsakanin al´adu dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/BvUL

An dai kammala wannan babban taro a kan addinin Islama da ya gudana a fadar shugaban tarayyar Austria dake birnin Vienna ba da wani kace nace ba.

Shugaban al´umar musulmin kasar ta Austria Anas Shakfeh ya ce ra´ayin dukkan wadanda suka yi jawabi a wajen taron ya zo daya cewa ba wata mazhaba a cikin addinin Islama da ta amince da ta´addanci da tsattsauran ra´ayi. Shakfeh ya nunar da cewa kasashen musulmi na amfani da addinin na Islama don cimma wani buri na dadam yayin da su kuma kasashen yamma ke nunawa mabiya wannan addini bambamci.

“Nuna wariya da rashin yarda sun dabaibaye wannan dangantaka, hakan kuwa ya zama wata shaida dake tabbatar da muhimancin daukar wannan mataki da makamantansa.”

Gwamnatin tarayyar Austria dai ba ta gayyaci kungiyoyi masu tsattsauran ra´ayi ba. A saboda haka wasu mahalarta taron suka yi sukar cewa taron zai amfanad da wadanda a da dama ba sa bukata shi. Hakazalika ba kowa ne ya amince da shawararin da aka yi ba. Tun da farko kuwa masu shirya taron sun ce ba za su fid da sanarwar bayan taro ba.

A jawabin sa ministan kula da al´amuran addini na kasar Masar, Mahmoud Zakzouk tuni yayi cewar tun a cikin karni na 14 addinin Islama ya waye da manufofin na demukiradiya da zamantakewa tsakanin masu bin al´adu iri dabam-dabam. A lokaci daya ministan yayi korafi game da farfagandar nuna kyamar addinin Islama da ake yadawa a cikin kasashen yamma.

“Ba laifi ba ne idan aka nunawa musulmi daraja ko kuma muhimmancin wannnan zamani na hadewar manufofin kasashe, amma musulmi suna adawa duk wata manufa ta nuna karfi akan su.”

Daga cikin wadanda suka yi jawabi a gun taron mai taken Addinin Islama a cikin wata duniya mai al´umomi da al´adu dabam-dabam, har da shugaban Iraqi Jalal Talabani da takwaransa na Afghanistan Hamid Karzai. Karzai ya ce ba tsattsauran ra´ayi ne kadai barazana ga zamantakewar al´adu dabam-dabam ba, a´a matsalolin rayuwa kamar talauci da rashin aikin yi na taka rawa bisa manufa.

Austria dai na daukar kanta a mastayin mai yin sulhu tsakanin al´adu dabam-dabam. Saboda haka a cikin jawabinsa na bude taron shugaba Heinz Fischer ya yi tuni da cewa bisa al´ada kasar sa na tafiyar da wata kyakkyauwar dangantaka da Islama. Tun kimanin shekaru 90 da suka wuce aka amince da kungiyar musulmi a cikin kasar. Kuma kawo yanzu ana zaman cude-ni in cude-ka a tsakani.

“A dangane da rikice-rikicen da ake yi da musulmi, babu wani lokaci da ya kai yanzu muhimmanci wajen gudanar da irin wadannan tarurruka don samar da fahimtar juna tare da gano hanyoyin warware matsalolin da ake fuskanta a wannan zamani.”

Duk da suka da kakkausan lafazi da shugaban jam´iyar masu ra´ayin rikau a Austria yayi da cewa taron wata gurguwar dabara ce, ministar harkokin waje Ursula Plassnik ba ta ko kula ba, hasali ma cewa ta yi kasar zata kira wani taron limaman addinin Islama bayan ta karbi ragamar shugabancin KTT nan da makonni 6 masu zuwa.