1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron kolin kungiyar EU a birnin Brussels.

Mohammad Nasiru AwalMarch 27, 2004
https://p.dw.com/p/Bvl0

Tun a gun taron kolinsu na birnin Lisbon shekaru 4 da suka wuce, shugabannin gwamnatoci da na kasashen KTT EU sun kuduri aniyar mayar da nahiyar Turai ta zama ja gaba a karfin tattalin arziki kafin shekara ta 2010, to amma bisa ga dukkan alamu ba za´a cimma wannan buri ba, sakamakon matsalolin marasa aikin yi da koma-bayan tattalin arziki da kuma karuwar tsofaffi da ake samu a kasashen nahiyar Turai. Haka zalika daukacin kasashe membobin kungiyar da hukumarta da kuma majalisar ta suna korafi game da tafiyar hawainiya da ake samu bisa manufar daukar matakan yin sauye-sauye. Shugaban majalisar Turai Pat Cox ya nunar da cewa:

"Yau shekaru hudu kenan da muka faro amma har yanzu ba mu cimma wani abin a zo a gani ba. Ana samun jinkiri wajen aiwatar da manufofin da muka sa a gaba, saboda haka muna yia fadawa cikin wani hali na rashin yarda."

Sanarwar bayan taron dai ta yi kira da a mayar da hankali wajen ta da komadar tattalin arziki tare da kirkiro sabbin guraben aikin yi. Don ta haka ne kawai za´a iya farfado da tattalin arziki kasashen kungiyar don daidaita kasafin kudinta. A dangane da matsalar nan ta karuwar tsofaffi a Turai, dole a yiwa tsarin fansho da na kiwon lafiya gyaran fuska.

Don bawa masana´antun Turai damar shiga tserereniyar ciniki da takwarorinsu na duniya, dole kasashen kungiyar EU su dauki sahihan matakan farfado da tattalin arzikinsu. Don cimma wannan manufa kasashen Jamus, Faransa da kuma Britaniya sun ba da shawarar kirkiro wani mukami na babban kwamishina wanda zai rika kula da batutuwan tattalin arziki, kamar yadda shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya nunar:

"Muna bukatar wani jagora a cikin hukumar EU, wanda zai samu matsayi shigen na mataimakin shugaba don kula da manufofin tattalin arziki."

A ranar farko ta taron batun yaki da ta´addanci a cikin kasashen kungiyar EU da kuma na kundin tsarin mulkin kungiyar suka mamaye zauren taron. Shugabannin sun tsayar da ranar 11 ga watan maris ta kasance ranar tunawa da wadanda hare-haren ta´adancin birnin Madrid suka rutsa da su. Kana kuma sun zartas da kudurori da dama da nufin yakar ta´addanci, inda aka nada dan kasar Holland Gijs de Vries a matsayin babban jami´i da zai rika kula da musayar bayanai da inganta hadin kai tsakanin ´yan sanda da hukumomin leken asiri. To amma shawarar da aka bayar ta kafa wata hukumar leken asiri ta bai daya shigen ta kasar Amirka ba ta samun karbuwa ba.

Taron ya kuma amince da wani sashe na kundin tsarin mulkin kungiyar EU, wanda ya tanadi baiwa duk wata kasa ta kungiyar da ta fuskanci harin ta´addanci, taimakon soji. Wani muhimmin abu da taron ya cimma, shine game da kundin tsarin mulkin kungiyar nan gaba. Bayan da kasashen Spain da kuma Poland suka janye adawar da suka nunawa wani sashe na tsarin mulkin, yanzu an samu kyakkyawan yanayi na rattaba hannu kan tsarin mulkin a gun taron kolin da kungiyar ta EU zata yi a ran 17 ga watan yuni. Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya bayyana wannan ci-gaban da cewa babbar nasara ce ga kungiyar EU.