1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Kammala Taron Kungiyar OSCE

April 29, 2004

A yau aka kammala taron yini biyu da kungiyar tsaro da hadin kai a nahiyar Turai da aka gudanar a birnin Berlin domin bitar matsalar kyamar Yahudawa da sauran manufofi na wariyar jinsi da banbancin addini

https://p.dw.com/p/Bvk7
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin jawabinsa ga taron kungiyar OSCE a Berlin
Ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer lokacin jawabinsa ga taron kungiyar OSCE a BerlinHoto: AP

A lokacin da yake jawabin rufe taron na kungiyar tsaro da hadin kai a nahiyar Turai OSCE, ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ce wajibi ne a ci gaba da daukar nagartattun matakai domin yaki da manufar kyamar Yahudawa musamman ta la’akari da ta’asar kisan kare dangin da Yahudawa a nahiyar Turai suka fuskanta a karni na 20 da ya gabata. Wannan ta’asa mai kama da gigin barci ta sanya ya zama wajibi akan kasashen Turai baki dayansu su dauki matakan yaki da manufar kyamar Yahudawa da wariyar jinsi, manufar da ba ta da wata kyakkyawar makoma a duniyar nan dake dada zama rufa daya. A cikin sanarwar bayan taron da suka bayar, kasashen kungiyar ta OSCE sun yi alkawarin yin Allah waddai da duk wata manufa ta adawa da Yahudawa da wariyar jinsi a dukkan bangarori na rayuwa. Za a gabatar da shirye-shirye na ilimantarwa da wayar da kan matasa domin kare su daga irin wannan akida ta rashin hakuri da juna. Kasashen sun bayyana damuwarsu da yadda ake amfani da hanyar sadarwa ta na’ura mai kwakwalwa Internet domin yada akidar kyamar yahudawa zuwa sauran sassa na duniya. Matasa sune suka fi fuskantar barazanar rungumar wannan akida, inda ake fafutukar cusa ta a zukatansu in ji ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer, wanda kuma ya kara da cewar:

Girmama hakin dan-Adam wajibi ne akan kowa-da-kowa. Ita kuma akidar kyamar Yahudawa wata manufa ce dake da nufin hana zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin jama’a masu banbancin al’adu da akidar addini ko launin fata tare da fatali da mutuncin dan-Adam.

Kungiyar ta OSCE ta yanke kudurin karfafa musayar rahotanni tsakanin kasashenta. Nan gaba wata cibiyar kula da manufofin demokradiyya da zata kafa a birnin Warsaw ita ce zata rika tara rahotanni da bayanai na farfaganda ko hare-hare da sauran miyagun laifuka dake da nasaba da kyamar Yahudawa da wariyar jinsi. To sai dai kuma gabatar da kuduri kawai ba zai tsinana kome ba sai an hada da gabatar da nagartattun matakai da kuma hadin kai da kungiyoyi masu zaman kansu in ji Joschka Fischer.

A lokacin wata liyafar da ya shirya wa mahalarta taron, shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya ce ba za a iya dora wa ‚yan sanda kawai alhakin yaki da manufar adawa da Yahudawa ba. Abu mafi alheri shi ne a bude wani babi na tattaunawa da musayar yawu tsakanin dukkan mutanen da lamarin ya shafa ba tare da rufa-rufa ba. Gudanar da taron da aka yi a Berlin abu ne dake yin nuni da irin ci gaban da aka samu a fafutukar murkushe akidar adawa da Yahudawa da wariyar jinsi da banbance-banbance na addini da al’adu in ji Schröder.