1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An karrama 'yan Afirka bisa kokarinsu na kare muhalli

May 23, 2018

Gerald Bigurube na Tanzaniya da Clovis Razafimalala na Madagaska da suka sadaukar da rayuwar su wajen ganin albarkatun kasar da ke kasashen su sun tsira daga gurbacewa sun sami lambar girmamawa ta kasar Jamus a Afrika.

https://p.dw.com/p/2yCiH
Global Ideas Südafrika Eukalypten
Hoto: picture-alliance/blickwinkel/J. Hauke

Shekaru 44 Gerald Bigurube mai shekaru 66 dan kasar Tanzaniya ya sadaukar don ganin dabbobin dawan dake kasarsa ta Tanzaniya da kuma muhalli sun tsira daga barazanar da suke fuskanta a nahiyar Afrika baki daya, a matsayinsa na dadadden shugaban hukumar kula da gidan ajiyar dabbobin kasar watau TANAPA,  ya jagoranci yaki da fataucin hauren giwa, ya kasance daya daga cikin wadanda suka shige gaba wajen tabbatar da ingantar gandun daji da muhalli a Tanzaniya har sai da kasar ta yi nasarar samun makudan kudade a fannin 'yan yawon bude ido.

Deutsche Afrika Stiftung Pressebild | Gerald Bigurube & Detlef Wächter
Gerald Bigurube na kasar Tanzaniya da Detlef WächterHoto: Deutsche Afrika Stiftung

Shi kuwa Clovis Razafimalala na kasar Madagaska ya shiga harkar tsare gandun daji  da muhallin ne daga baya inda ya yi shura wajen ganin dazuzzukan dake kasar Madagaska sun tsira daga barazanar da ke illata su, sakamkon wannan gudummwa da wadannan mutane suka bayar a bana, gungun jagororin gidauniyar kasar Jamus a Afrika wacce ta kunshi wasu kwararru a fanni daban daban na duniya suka zabesu don samun lambar girmamawa ta Gidauniyar.

Deutsche Afrika Stiftung Pressebild | Clovis Razafimalala & Marcus Schneider
Clovis Razafimalala na kasar Madagaska da ya karbi kyautar tare da Marcus Schneider Hoto: Deutsche Afrika Stiftung

Koyaushe ana son samun wadanda za su kare muhalli tun daga tushe, mutanen da ke kishin kare dazuka kasashensu. Wannan ba shi bane karon farko da ake karrama 'yan asalin Afrika da lambar girmamawa ta kasar Jamus ba, don kuwa 'yan kasashe kamar Yuganda da Afirka ta Kudu gami da Tunisiya sun taba samun lambar a baya.