1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe daya daga cikin wadanda ake zargi da harin Boston

April 19, 2013

Jami'an tsaron Kasar Amurka sun bayyana sunayen wadanda ake zargi da kai hari yayin gudun fanfalake na Marathon a Boston.

https://p.dw.com/p/18JZ8
Wadanda ake zargi da kai hari a Boston na Amurka.Hoto: Reuters

An kashe daya daga cikin mutane biyun da ake zargi da kai hari a yayin gudun fanfalaki na Marathon da aka gudanar a Birnin Boston, a wata musayar wuta da su kayi da Jami'an tsaro a kauyen Watertown dake kusa da Birnin na Boston.

Jami'an tsaron Amurka sun bayyana cewa mutanen biyu suna da alaka da kasashen Duniya da kuma horo kan aikin soja, sannan kuma 'yan uwan Juna ne da suka fito daga yankin Chechiniya na kasar Rasha, kuma anfi sanin su da sunan mahaifinsu Tsarnaez.

Wata kafar yada labarai ta Kasar Amurka ta ruwaito cewa 'yan uwan da ke da shekaru 26 da kuma 19 suna da takardun zama a Amurkan na din- din -din kuma suna zaune a kasar tun tsahon shekara guda data gabata.

Ya zuwa yanzu dai Jami'an 'yansanda a Birnin Boston na gudanar da binciken gida gida domin gano wanda ake zargi na biyu dan kimanin shekaru 19 a duniya mai suna Dzhokhar Tsarnaev bayan da aka kashe danuwansa mai shekaru 26 da haiahuwa Tamerlan Tsarnaev da sanyin safiyar yau.

Sai dai kuma Mahaifin wadanda ake zargin Anzor Tsarnaev ya bayyana karamin dan nasa da ake nema ruwa a Jallo da haziki kuma nutsatstsen yaro.

A wani labarin kuma wani dan sanda ya rasa ransa yayin da wani kuma ya samu munana raunuka bayan da aka kai hari a wata jami'a kusa da Birnin na Boston. Ya zuwa yanzu yansanda sun ce basu gano dalilin kai wannan harin ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe