1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane a ƙalla 185 a Najeriya

April 22, 2013

An gwabza faɗa tsakanin sojoji da 'yan ƙungiyar Boko Haram a garin Baga dake kan iyaka da Chadi cikin jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/18KOt
In this Wednesday, Sept. 28, 2011 photo, police officers armed with AK-47 rifles stand guard at sandbagged bunkers along a major road in Maiduguri, Nigeria. The radical sect Boko Haram, which in August 2011 bombed the United Nations headquarters in Nigeria, is the gravest security threat to Africa's most populous nation and is gaining prominence. A security agency crackdown, which human rights activists say has left innocent civilians dead, could be winning the insurgency even more supporters. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: dapd

An bada rahoton cewa mutane sama da 150 suka mutu a sanadin faɗan. Masu aiko da rahotanni sun ce an kwashe awoyi ana yin bata kashi tsakanin maharan da sojojin abin da ya tilasta wa mutane da yawa tserewa daga yankin.

Kuma baya ga asarar rayukan jama'a da aka samu, an ƙona gidaje da motoci da kuma kamfanoni da dama. Wani wanda ya gane wa idonsa abin da ya faru ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, cewar hukumomin yankin sun binne gawarwakin mutane a ƙalla 185 a ranar Lahadi. Wannan al'amari ya faru ne a daidai lokacin da gwamnatin Tarrayar Najeriya ta ba da sanarwar girka wani kwamiti, wanda zai tattauna batun yin afuwa ga 'yan ƙungiyar Boko Haram domin samar da zaman lafiya a Najeriyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal