1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wani komandan na Aqmi a Mali

March 1, 2013

A ci-gaba da farautar masu kaifin kishin addini a arewacin Mali,dakarun kasa da kasa sun kashe Abdelhamid Abu Zayid wani komandan na Aqmi a wani artabu a cikin tsaunikan Ifoghas

https://p.dw.com/p/17oSN
Aldelhamid Abu ZayidHoto: DW/J.M. Oumar

Wata sanarwa da gidan talabijan na kasar Aljeriya Ennadar ta bayana,dakarun kasa da kasa dake ci-gaba da gobza fada da kungiyoyin kishi islamam a arewacin Mali,sun samu nasarar halaka Abdelhamid Abu Zaiyid wani babban komandan na kungiyar alqa'ida a yankin Magreb a yayin wani artabu a cikin tsunikan Ifoghas dake arewacin na Mali.
Sanarwar ta kara da cewar an yi wannan aragamar ne a ranar Talatan nan da ta gabata inda a kalla masu kishin islama 40 ne suka rasa rayukansu ,yayinda aka lalata wata ma'ajiyar makamai a cikin tsaunukan
Shi dai Albdulhamid Abu Zayid,shi ne ya jagoranci kamun garin Tombuktu har tsawon watani goma,shi ne kuma mutunen da ake ganin keda mumunar akida inda ya kaddamar da shari'a ta hanyar datse hannuwa,da duka da kuma azabatar da masu laifi a musulunce. Sannan ana zargin sa da jagorantar satar wasu ma'aikatan Areva 'yan kasar Faransa a garin Arlit dake arewacin jamhuriyar Nijer a shekara ta 2009.
Yanzu haka dai ana can ana wani artabun a wani tsibiri dake kan kogin Nijer kusa ga garin Gao, inda aka bada sanarwar wasu 'yan kishin islaman sun buya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi