1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan sanda a Masar

February 19, 2019

Hukumomi a Masar, sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Alkahira, ya halaka jami'an 'yan sanda akalla uku.

https://p.dw.com/p/3Df7h
Kairo Bombenanschlag
Hoto: Reuters/M. Abd El Ghany

A cewar ma'aikatar tsaron kasar ta Masar, harin wanda aka kai shi da yammacin jiya Litinin ya faru ne a kusa da masallacin nan mai tarihi wato Al-Azhar.

Akwai ma wasu jami'an 'yan sanda biyu da suka jikkata a lamarin.

Wani faifan bidiyo da aka wallafa da safiyar yau Talata, ya nuno 'yan sandan sun taso keyar maharin kafin daga bisani ya tayar da nakiyar da ke a jikinsa.

Da ma dai jami'an na kokarin kama mutumin ne a farautar wasu da ake zargi da kai hari kusa da wani masallacin a birnin Giza a ranar Juma'ar da ta gabata.